Ƙungiyar IPMAN ta janye yakin aikin da ta shirya tsunduma
Ƙungiyar dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN, ta buƙaci mambobinta da su ci gaba da sayar da Fetur kamar yadda suka saba.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar a daren yau Talata mai ɗauke da sahannun shugabanta Mohammed Kuluwa,.
Sanarwar ta ce, “Bayan tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki, muna umartar gidajen mai da su buɗe tare da ci gaba da sayar da man fetur yayin da uwar kungiya za ta ci gaba da tattaunawa,”
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan umarnin farko da ƙungiyar ta bai wa mambobinta na su rufe ilahirin gidajen man fetur a faɗin Najeriya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, yanzu haka ƴan Najeriya na fama da tsadar fetur a kusan dukkan jihohi inda a wasu wuraren ya haura Naira 370 a kan kowacce lita guda, yayin da a wasu Jihohin kuma ake sayar da lita guda a kan fiye da Naira 400.