Connect with us

Labarai

EFCC Ta Kama Wani Mutum Da Kudin Da Ta Yi Zargin Na Sayen Kuri’u Ne

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani mutum dauke da sabbin takardun kudi na Naira miliyan 30, wanda ya saba wa sabon tsarin jayyade kudi wanda ya ba kowane mutum damar rike Naira 100,000 kacal.

Shugaban Hukumar, AbdulRasheed Bawa ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a wani shirin gidan talabijin na TVC mai suna Your Veiws wanda jaridar SOLACEBASE ta bibiye shi.

Bawa ya ce tsarin na kayyade rike tsabar kudi ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu sauki wajen gano kudaden domin babban bankin Kasa na da jerin lambobin duk sabbin takardun kudi na Naira da yadda aka fitar da su da kuma wadanda ke da damar yin amfani da su.

“Mun kama wani mutum a ranar Alhamis dauke da sabbin naira miliyan 30 wanda muke binciken yadda mutumin ya samu irin wannan tsabar kudi, saboda tsarin kayyade tsabar kudi ya ba da damar rike Naira 100,000 kawai,” in ji Bawa.

Shugaban na EFCC ya ce duk da cewa da dama na korafin yadda ake fama da matsalar samun kudi nan take, hukumar na hada kai da babban bankin Kasa CBN domin sanya ido kan yadda ake raba sabbin kudaden na naira ga bankuna da kuma tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu kudaden kamar yadda doka ta tanada kuma ta hana tarasu.

Ya yi nuni da cewa, manufar tana rage sayen kuri’u tuni kuma hakan zai tabbatar da cewa zaben 2023 ya yi fice a zaben da aka yi amfani da shi wajen kashe kudi kadan.

“Manufar rashin kudi ba ta nufin kawar da siyan kuri’u kadai ba saboda ana sa ran zai haifar da natsuwa a cikin tattalin arzikinmu.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet