Labarai
Yadda ɗan takarar APC Bola Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa ta Awolowo da ke Falomo a jihar Lagos.
Rahotonni sun bayyana cewa ɗan takarar ya isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe tare da mai ɗakinsa Oluremi Tinubu.
Sai dai BBC ta ruwaito cewa, An samu jinkiri gabanin fara kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓen, sai dai daga baya zaɓen ya kankama.
Haka kuma ta bayyana cewa, Akwai mutum aƙalla 832 da suka yi rajistarsu a wannan rumfar zaɓe.