Labarai
Kowa ya tabbatar ya zaɓi shugaban da ya dace- Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa l Muhammadu Buhari, yi kira ga ƴan Najeriya da su tabbatar da cewa sun zaɓi shugabannin da suka cancanta.
Shugaban ya yi jan hankalin ne da safiyar yau Asabar ta cikin jawabinsa bayan da ya kammala kaɗa ƙuri’arsa ya kaɗa ƙur garin Daura da ke jihar Katsina.
Shugaba Buhari, ya kuma bayyana cewa zaɓar waɗanda suka dace shi ne mafita ga al’ummar Najeriya.
Muhammadu Buhari, ya fito ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe inda ya kaɗa ƙuri’a tare da mai uwar gida Hajiya A’isha Buhari.