Connect with us

Labarai

Hukumar ICPC Ta Kama Wani Mutum Da Tsabar Kudin Miliyan 2 A Bauchi

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ICPC ta kama wani mutum dauke da tsofaffi da sabbin naira miliyan biyu a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Wanda ake zargin, Hassan Ahmad, an kama shi ne a ranar Juma’a da kudin a cikin jakar ‘Ghana Must Go’ a lokacin da yake tuka wata mota kirar Hilux.

An kama shi yana kan hanyarsa ta zuwa Gombe daga jihar Bauchi. Ana zargin za a kai wa wani dan siyasa kudin.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, @icpcnigeria, mai taken: “ICPC ta kama wani dan siyasa da Naira miliyan 2.”

Ya ce sojojin na 33 Artillery Brigade code mai suna: Operation Safe Conduct da aka tura karamar hukumar Alkaleri Bauchi ne suka kama wanda ake zargin, kuma aka mika shi ga ICPC.

A cewar hukumar, wanda ake zargin ya mallaki sabbin takardun kudi Naira 900,000 da tsofaffin takardun kudi naira miliyan 1.1.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Sai dai hukumar ba ta bayyana sunan dan siyasar ba.

Ya ci gaba da cewa: “Ofishin ICPC na jihar Bauchi ya kama wani Hassan Ahmad da ke da kudi naira miliyan biyu na tsofaffi da kuma sabbin kudade a cikin halin kuncin da ake ciki a kasar nan.

“Rundunar Sojoji na 33 Artillery Brigade Operation Safe Conduct da aka tura Alkaleri a jihar Bauchi sun kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a, kuma sun mika shi ga ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Bauchi.

“Ahmad ya mallaki tsabar kudi Naira 900,000 a sabbin takardun kudi na naira da kuma naira miliyan 1.1 na tsofaffin kudade kuma ana kai kudaden ne a wata mota kirar Hilux baka mai lamba JMA 85 AZ.

“Kudaden wadanda aka zuba a cikin jakar ‘Ghana Must Go’, sun hada da dauri shida na sabbin kudi naira dubu daya na Naira 600,000; dam shida na sabbin kudi naira dari biyar na naira 300,000, da kuma tsofaffin naira dari biyu na naira miliyan 1.1.

“Wanda ake zargin ya amsa cewa zai kai kudaden ne jihar Gombe ga wani dan siyasa.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet