Labarai
Wata Gobara Ta Kone Sassan Babbar Kasuwar Maiduguri

Babban Kasuwar Maiduguri da aka fi sani da Monday market ta kama da wuta.
Har yanzu gobarar da ta tashi a safiyar Lahadin nan tana ci gaba da ruruwa inda jami’an kashe gobara ke fafutuka domin shawo kan lamarin.
Daraktan hukumar kashe gobara na jihar, Umaru Kirawa wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa afkuwar lamarin, ya ce hukumar kashe gobara ta jihar, da ta tarayya da sauran hukumomin kashe gobara daga cibiyoyi daban-daban sun hada kai domin dakile gobarar.
“Mun tura jami’ai domin shawo kan lamarin,” in ji Kirawa. (NAN)