Connect with us

Labarai

Mutane Biyu Sun Kone A Wani Hari Da Aka Kai Ofishin Jam’iyyar NNPP Na Kano

Mutane biyu sun mutu a ranar Lahadi a wani hari da aka kai ofishin yakin neman zaben dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar NNPP a jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Abdullahi Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce wasu gungun ‘yan daba sun bankawa ofishin wuta tare da wasu mutane biyu da ba a san ko su wanene ba a cikin wata mota dake tsaye a cikin ginin ta kone kurmus.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu rahoton faruwar lamarin da misalin karfe 4 na yamma yayin tattara sakamakon zabe a ofishin INEC da ke karamar hukumar Tudun Wada.

A cewar Kiyawa, ‘yan bangar sun kuma yi yunkurin tare hanyar zuwa ofishin INEC.

“Nan da nan aka tattara jami’an tsaro zuwa wurin,” in ji PPRO. “Daya daga cikin ‘yan barandan ya samu mummunan rauni kuma an garzaya da shi asibiti inda ya mutu a lokacin da yake karbar magani.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, Da yake lura da cewa ana gudanar da bincike, ya kara da cewa “an kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan daba ne.”

A wani lamari makamancin haka, ‘yan sanda sun dakile yunkurin kona ofishin INEC da ke karamar hukumar Takai yayin da ake tattara sakamakon zabe.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 2:30 na rana.

Kiyawa ya bayyana cewa, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, a cikin gaggawar mayar da martani, sun dakile harin, kuma an kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan dabae ne.

Sanarwar ta ce “An kammala tattara sakamakon cikin lumana kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet