Labarai
Obasanjo ya buƙaci shugaba Buhari ya soke zaɓen da aka yi

Tsohon shugaban ƙasa Chief Olusegun Obasanjo, ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya soke zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Obasanjo, ya buƙaci buƙaci hakan ne ta cikin wata wasika da ya rubuta mai ɗauke da kwanan watan jiya Litinin.
Ya ce, babu sahihanci a babban zaɓen da aka gudanar ranar Asabar ɗin, don haka zama wajibi a soke shi a yankunan da aka samu hatsaniya.
Chief Olusegun Obasanjo, Ya kuma buƙaci Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Najeriya daga faɗawa haɗarin rikici.