Connect with us

Labarai

INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Jihohi 20 Cikin 36 Na Kasar Nan

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, APC, Bola Tinubu ne ke kan gaba a sakamakon da INEC ke fitar wa na zaben shugaban Kasa daga jihohi.

Ya zuwa daren ranar Litinin ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana sakamakon zaben a jihohi 20.

Tinubu ne ke kan gaba da kuri’u 5,862,453, yayin da Atiku Abubakar na na m’iyyar PDP ya samu kuri’u 4,288,434 ya zuwa yanzu.

A halin yanzu Peter Obi na jam’iyyar Labour LP, yana matsayi na uku da 2,834,932; Rabiu Kwankwaso NNPP, ya samu kuri’u 1,315,549.

Wani abin sha’awa shi ne, Tinubu ne daya tilo wanda ya kasa samun nasara a jiharsa, inda ya sha kashi a hannun Obi a Legas. Atiku ya lashe zaben a jihar shugaban kasa  Muhammadu Buhari ta Katsina.

A yau ne ake sa ran gabatar da sakamakon wasu jihohi da kuma babban birnin tarayya FCT daga karfe 11 na safe.

Cibiyar taron kasa da kasa, ICC, da ke Abuja, wurin da ake gudanar da taron kasa, na ci gaba da fuskantar tsauraran matakan tsaro.

‘Yan adawa a ranar Litinin sun yi kira da a dakatar da bayyana sakamakon zaben. Dino Melaye na PDP da Emeka Ihedioha a wani lokaci sun fice daga ɗakin tattara sakamakon Shugaban Ƙasa.

Jam’iyyun dai sun koka da yadda ake tafka kura-kurai, da yawan kuri’u, da kin sanya sakamakon da jami’ai suka yi a shafin na INEC, da dai sauransu.

Binciken da DAILY POST ta yi ya nuna cewa daga cikin rumfunan zabe 176,846 da ke kananan hukumomi 774, sakamakon da aka gabatar sun fito ne daga rumfuna 79,673.

Ga Sakamakon  jihohin 20:

KWARA
*Tinubu – 263,572*
Peter Obi – 31,116
Atiku – 136,909

OSUN
Tinubu – 343,945
Obi – 23,283
*Atiku – 354,366*

ONDO
*Tinubu – 369,924*
Obi – 47,350
Atiku – 115,463

OGUN
*Tinubu – 341,554*
Obi – 85,829
Atiku – 123,831

OYO
*Tinubu – 449,884*
Obi – 99,110
Atiku – 182,977

ENUGU
Tinubu – 4,772
*Obi – 428,640*
Atiku – 15,749

GOMBE
Tinubu – 146,977
Obi – 26,160
*Atiku – 319,123*

JIGAWA
*Tinubu – 421,390*
Obi – 1,889
Atiku – 386,587

ADAMAWA
Tinubu – 182,881
Obi – 105,648
*Atiku – 417,611*

KATSINA
Tinubu – 482,283
Obi – 6,376
*Atiku – 489,045*

NASARAWA
Tinubu – 172,922
*Obi – 191,361*
Atiku – 147,093

PLATEAU
Tinubu – 307,195
*Obi – 466,272*
Atiku – 243,808

BAUCHI
Tinubu – 316,694
Obi – 24,910
*Atiku – 426,607*

KANO
Tinubu – 517,341
Obi – 28,513
Atiku – 131,716
*Kwankwaso – 997,279*

EKITI
*Tinubu – 201,494*
Obi – 11,397
Atiku – 89,554

BENUE
*Tinubu – 310,469*
Obi – 208,372
Atiku – 130,081

LAGOS
Tinubu – 572,606
*Obi – 582,454*
Atiku – 75,750

YOBE
Tinubu – 151,459
Obi – 2,406
*Atiku – 198,567*

EDO
Tinubu – 144,471
*Obi – 331,163*
Atiku – 89,585

AKWA IBOM
Tinubu – 160,620
Obi – 132,683
*Atiku – 214,012

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet