Featured
Basaraken Gargajiya Ya Rasu Tare Da Ƴaƴansa 3

Hakimin Basirka Dan Amar na masarautar Dutsan jihar jigawa Alhaji Muhammad Suleiman ya rasu
Basaraken ya rasu tare da ƴaƴansa uku bayan afkuwar hadarin mota akan hanyar sa ta zuwa Gwaram.
Sai dai matarsa da yayansa biyu ne suka tsallake kamar yanda Sarkin yakin Dutse ya bayyana.
Tuni dai aka yi jana’izar su kamar yanda addinin musulunci ya tanadar.