Labarai
Kotu ta yanke wa su Murja Kunya hukuncin Talala

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke Hausawa filin Hokey a Kano, ta yanke wa fitacciyar matashiyar nan a kafar Tiktok Murja Ibrahim Kunya da abokan burminta hukuncin Talala.
Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Halliru, ta yanke wa Murja Ibrahim Kunya hukuncin ɗaurin Talala na sharar Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad na tsawon sati uku.
Haka kuma matashiyar za ta riƙa zuwa hukumar Hisba na tsawon watanni shida
Su ma abokan burminta Aminu BBC da Ashuru Idris wanda aka fi sani da Mai wushirya da kuma Sadik Sharif za su riƙa yin sharar masallacin Juma’a Murtala har tsawon sati uku.
Tun a baya dai kotun ta aike da matasan zuwa gidan gyaran hali ne bisa zargin su da yin abubuwan da ba su dace ba a dandalin Tiktok.