Featured
Kotu Ta Yankewa Murja Kunya Hukuncin Sharar Asibitin Murtala

Kotun Shari’ar Musulunci dake zaman ta a filin Hokey, ta yankewa Murja Ibrahim Kunya hukuncin sharar Asibitin Murtala na tsahon sati uku, tare da yin bidiyo na neman afuwar Al’umma cikin kwanaki biyu kan abinda ta aikata
Kazalika kotun ta yankewa Idris Ashiru mai wushirya da Aminu Ibrahim BBC da Sadik Sharif Umar hukunci share Masallacin Murtala na tsahon makonni uku.