Connect with us

Labarai

Rivers: INEC Ta Bayyana Wadanda Suka Lashe Zaben Majalisar Wakilai

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a jihar Ribas ta saki sunayen wadanda suka lashe zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a Rivers.

INEC ta sanar da sakamakon ne a wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Misis Geraldine Ekelemu, ta raba wa manema labarai a Fatakwal ranar Asabar.

Hukumar ta sanar da wanda ya lashe zaben Sanatan Ribas ta Kudu-maso-Gabas a matsayin Mpigi Barinada na PDP da kuri’u 53,734 inda ya doke abokin takararsa na APC Ngofa Nyimenuate wanda ya samu kuri’u 24,123.

An bayyana cewa Sanatan Rivers ta Yamma ya samu nasara a hannun Banigo Harry na PDP wanda ya samu kuri’u 67,668 inda ya doke Asita Asita ta APC wadda ta samu kuri’u 32,572.

Hukumar ta kuma sanar da cewa, Onyesoh Allwell na PDP ya lashe kujerar Sanatan Rivers ta Gabas da kuri’u 134,283 inda dan takarar LP Benjamin Okwuwolu ya samu kuri’u 74,725.

Hakazalika, INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan majalisar wakilai daga Okrika/Ogubuolo, Etche/Omuma, Ikwere/Emohua, Ahoada West/Ogba/Egbema/Ndoni, Akuku-Toru/Asari-Toru, Eleme/Tai/Oyibo, Abua- Uduah/Ahoada Gabas, Andoni-Opobo/Nkuru, Degema/Bonny, Obio/Akpor, da Fatakwal 1, yayin da aka dakatar da sakamakon Port Harcourt 2.

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APC ta lashe kujerar Okrika/Ogubuolo ne kawai, yayin da jam’iyyar PDP ta samu kujeru tara sannan jam’iyyar Labour kuma ta samu kujera daya kacal a mazabar tarayya ta Port Harcourt 1.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa Rivers na da mambobi 12 a zauren majalisar dokokin kasar.

Jaridar Solacebace ta tuna cewa tun da farko kwamishinan zabe na jihar Dr Johnson Alalibo ya shaidawa manema labarai cewa za a dakatar da sake duba sakamakon zaben mazabar tarayya ta Fatakwal 2 saboda rahotannin da aka samu. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet