Labarai
Da Dumi-Duminsa: INEC Ta Ayyana Dan Takarar APC A Matsayin Wanda Laahe Zabe A Sokoto

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Aliyu Ahmed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Sokoto.
Aliyu Ahmed ya samu kuri’u 453,661 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Umar Sa’idu na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 404,632.
An gudanar da zaben ne a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023, yayin da INEC ta bayyana sakamakon a ranar Litinin 20 ga wata.