Labarai
Gwamna Bala Muhammad ya sake lashe zaɓe

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulƙadir, na jam’iyyar PDP ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar a zaɓen da aka ranar Asabar.
Shugaban tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, ne ya bayyana hakan yau Litinin.
Ya ce, Sanata Bala gwamna mai ci kuma Ƙaura Bauchi, shi ne ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280.
Haka kuma, Ya bayyana Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 432,272.