Labarai
Yayin da APC ke shirin gudanar da Zanga-zanga a Kano: An baza ƴan sanda a sassan jihar

Rundundar ƴan sandan jihar Kano ta baza jami’ai da dama a sassa daban daban Yan sanda a wurare dabam-daban a ƙwarya birnin jihar da safiyar yau Laraba.
Hakan dai ya biyo bayan shirin gudanar da zanga-zangar lumana da jam’iyyar APC ta shirya yi domin nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan da INEC ta sanar
Rahotonni sun nana cewa jami’an tsaron cikin shirin ko ta kwana an jibgesu ne a ɓangarorin jihar Kano da dama.
A jiya Talata ne jam’iyyar ta magantu kan sakamakon ta bakin lauyanta Barista Abdul Fagge tana mai nuna ƙin amincewa da sakamakon tare da shan alwashin garzawa kotu nan da mako guda matuƙar INEC ba ta bayyana sakamakon a matsayin wanda bai kammalu.