Labarai
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Cewa Akwai Aikin Tsaftar Muhalli A Gobe Asabar

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatarwa da al’ummar jihar Gobe akwai tsaftar muhalli ta karshen wata da aka saba gudanarwa.
Haka Kuma Gwamnatin jihar ta Kano ta buƙaci al’umma musamman masu baburan Adaidaita Sahu da su guji karya dokar tsaftar muhalli da ake gudanarwa Duk Karshen wata.
Kwamishinan muhalli na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya sanar da hakan ga manema labarai inda ya Buƙaci Hadin Kan al’ummar Jihar Kano domin samun Nasarar shirin.
Haka Kuma akwai Kotun tafi da Gidanka wadda aka Samar Domin Hukunta masu Kunnen Kashi, dakan bijirewa dokar wajen fitowa harkokin su.