Connect with us

Labarai

Zaɓen Gwamna: INEC Ta Kammala Dora Sakamakon Zaɓen Wasu Jihohi

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa ta kammala dora sakamakon zaben gwamnan jihar Borno da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta saka 138,124 daga cikin sakamakon zabe 149,263 da ake sa rai a yanar gizo.

Sakamakon da aka dora ya ƙunshi kashi 93 cikin 100 na sakamakon zaɓen gwamna na 2023 gabadaya.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa jam’iyyun adawa da wasu ‘yan Najeriya sun caccaki INEC kan gazawarta wajen saka sakamakon zaben nan take a lokacin zaben shugaban kasa.

Ko da yake hukumar ta yi bayanin cewa akwai kura-kurai da aka samu wajen yada sakamakon zabe wanda da dama daga cikin masu suka suka ki amincewa da hakan.

Sai dai kwanaki kadan kafin zaben na ranar 18 ga watan Maris, INEC ta ce an gyara batutuwan fasahar tare da bayar da tabbacin cewa za a mika sakamakon zaben nan take.

Binciken da wakilinmu ya yi a ranar Asabar da karfe 9:45 na safe ya nuna cewa an loda sakamakon zaben daga jihohi 28. Sun hada da jihar Ogun, 5,015, (99%) an gabatar da sakamakon; Plateau, 4,984, (99%); Zamfara, 3,297, (93%); Yobe, 2,712, (96%); Taraba, 2,957 (82%); Sokoto, 3,805, (95%); Rivers, 6,300 (91%); Oyo, 6,387, (99%); Nijar, 4,621, (93%); Nasarawa, 3,242, (99%); Legas, 13,304, (99%); Kwara, 2,883, (99%); Kebbi, 3,674, (98%); Katsina, 6,588, (99%); Kano, 10,009, (89%); Kaduna, 7,578, (95%); Jigawa, 4,519, (99%); Gombe, 2,971, (99%); Enugu, 4,110, (99%); Ebonyi, 2,876, (97%); Delta, 5,858, (99%); Cross-River, 3,256, (99%); Borno, 5,071, (100%); Benue, 4,727, (93%); Bauchi, 5,110, (94%); Akwa-Ibom, 4,309, (99%); Adamawa, 3,967, (96%); da Abia, 3,994, (98%).

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet