Labarai
Mun cafke mutane 781 bisa aikata laifuka yayin zaɓe- Usman Alkali Baba

Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ec, Rundunar ta samu nasarar cafke mutane 781, bisa aikata laifukan da suka shafi harkokin zaɓe yayin zaɓukan bana da aka gudanar.
Babban sifeton ya bayyana hakan ne yau Litinin da yake ganawa da kwamishinonin rundunar na jihohi 36 da kuma wasu manyan jami’an ƴan sanda.
Usman Alkali Baba, ya ƙara da cewa, an aikata laifukan zaɓe har guda 145 a lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, wanda hakan ta sa rundunar ta cafke mutane 203.
Haka kuma ya ce, a lokacin zaɓen gwamnoni da ƴan majalisun dokokin jihohi, nan kuma an aikata laifuka 304, inda a wannan kuma, rundunar ta daƙume mutane 578.
BBC ta ruwaito cewa, Babban Sufeton ƴan sandan na Najeriya, Ya kuma yi Alla-wadai da ƴan siyasar da ke ƙoƙarin tayar da hargitsi ta hanyar tunzura jama’a domin cimma muradunsu.