Connect with us

Labarai

Zaben Gwamna: Yan Sanda A Sokoto Sun Kama Mutane 79 Bisa Zargin Aikata Wasu Laifuka

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto a ranar Lahadin ta ce jami’an tsaro sun kama mutane 79 da ake zargi da hannu a wasu laifuka a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan ya raba wa manema labarai a Sokoto, ta ce wadanda aka kama mutane ne da suka saba wa dokar takaita zirga-zirga da kuma wasu laifuka da suka saba wa dokar zabe.

Sanarwar ta kara da cewa, “Dukkan laifukan zaben da aka yi a cikinsu an yi cikakken bincike tare da mika su ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin gurfanar da su gaban kuliya.

Yayin da wasu da suka saba wa ka’idar dokar ‘yan sanda sun gurfanar da su gaban kotu. Sai dai kuma akwai wasu da ake ci gaba da bincike akan su.

A halin da ake ciki kuma, an ayyana Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.

Aliyu ya doke jam’iyyar PDP ne bayan ya samu kuri’u 453,661.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet