Kasuwanci
Bankin CBN Ya Tabbatar Da Sakin Biliyoyin Kudi Ga Bankunan Kasuwanci

Babban bankin Najeriya CBN ya ce kawo yanzu ya saki kudi masu yawan gaske ga Bankunan kasuwanci a kasar
A cewar bankin ya saki kudin ne ga Bankunan, domin su samu damar baiwa al’umma da suke tsananin bukatar kudin a hannu yanzu haka.
CBN ya ce daga ranar Alhamis ya fara sakin biliyoyin kudin ga Bankunan kasar, domin dai su sanya su a naurar cirar kudi ta ATM da nufin al’umma su samu.
Daga bisani ne kuma bankin ya bayar da umarnin bankuna su bude a karshen mako, domin dai baiwa al’umma dama su je domin samun kudin da zasu biya bukatun su.
Da alama kuma wannan umarni ya taimaka wajen saukakawa al’umma, domin kuwa a zagayen da KAKAKIHAUSA Time ta gudanar a wasu tituna na jihar Kano ta iske yadda Bankunan suka bude suna baiwa abokan hulɗar su damar shiga domin biya musu bukatun su.
Yawancin Bankunan dake kan titin zuwa Zariya a jihar Kano sun bude a karshen mako.