Connect with us

Ilimi

Shugaban ɗaliban YUMSUK ya buƙaci a ƙara yawan sabbin ɗaliban da ake wa gwajin lafiya

Sabon shugaban ɗaliban jami’ar Yusuf Maimuna Sule da ke birnin Kano Tafida Aliyu, ya buƙaci da a ƙara yawan adadin sababbin ɗaliban jami’ar waɗanda ake duba lafiyarsu a asibitin jami’ar da ke mazaunin ta na din-din-din.

Tafida ya yi wannan kira ne yayin wani zagayen ran-gadi da ya je asibitin yau Laraba domin ganin yadda aikin duba lafiyar ɗaliban ke gudana.

Wannann duba lafiyar dai ana yinsa ne ga dukkanin sababbin ɗaliban da aka bai wa gurbin karatu a jami’ar, domin tabbatar da cikakkiyar lafiyarsu kafin fara karatu.

A yayin ziyarar tasa Tafida ya tattauna da Jami’an lafiya na jami’ar da ke cikin makarantar domin ganin an ƙara adadin ɗaliban da ake dubawa a kowace rana domin ganin an sauƙaƙa wa ɗaliban wahalar Azumi.

Haka kuma, shugaban ɗaliban ya yi kira ga sababbin ɗaliban da su daina yin cincirindo a harabar jami’ar na din-din-din, maimakon haka wasu su riƙa zuwa ɗaya sashen duba lafiya na jami’ar wanda ke Ƙofar Nasarawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetjojobetcasibomcasibommatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetcasibomnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet