Labarai
Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyya iyalan Sheikh Al-Hussaini

Shugaban ƙasa Muhamadu Buhari, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh Al-Hussaini, shugaban kwamitin Fatawa na kwamitin kolin addinin musulunci, da aka fi sani da Shaykh Sharif Saleh, bisa rasuwar babban dansa Alhaji Musa Alkasim.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban a harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta ruwaito cewa, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na miƙa saƙon ta’aziyar ga malamin da gwamnati da kuma al’umma jihar Borno, rashin Marigayin.
Haka kuma sanarwar ta ce, shugaba Buhari, kaɗu matuƙa bayan samun rahoton rasuwar ta Alhaji Musa, tare da bayyana rashin nasa a matsayin abun jimami ga shehin malamin.
Buhari ya bayyana marigayi Alhaji Musa Alkasim mai shekara 59 a matsayin mutum mai halin dattako wanda za a dade ba manta da shi ba.
Haka kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi addu’ar neman gafara ga marigayin tare da fatan Allah ya bai wa iyalansa da al’ummar Borno hakurin jure rashinsa.