Labarai
Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 138

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 138 a gidan gwamnati.
Rahotonni sun bayyana cewa, gwamnan ya jagoranci aikin ne a daren jiya a daren jiya Lahadi.
A jawabinsa bayan musuluntar da mutanen maza da mata da suka fito daga karamar hukumar Sumaila gwamna Ganduje ya ja hankalinsu game da kulawa da Ibada tare da neman Ilimin addinin Musulinci.
Ganduje yayi kira ga wadanda suka musuluntar da su yi kokari wajen bin dokokin Allah SWT, tare da riko da koyarwar addinin na islama.
Wasu daga cikin wadanda suka karbi shahadar ta muslinci sun bayyana cewa wa’azin da sukeji a unguwanninsu a cikin Azumi ya taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalinsu su domin su shiga addinin.
Su ma wasu daga cikin su sun ce suna samun nutsuwa da addinin wanda hakan yasa suka amince su shiga domin su cigaba da gudanar da rayuwarsu akan tafarkin gaskiya da kuma tsari.
A yayin taron, an raba kayan Sallah ga wadanda suka musulunta maza da mata tare da raba musu jari domin su dogara da kansu.