Uncategorized
Tirela Makare Da Kaya Ta Auka Cikin Masallaci A Neja

A safiyar Talatar nan wata tirela da ke makare da kayan madare ta auka kan wani masallaci a yankin Suleja da ke Jihar Neja.
Tirelar ta auka cikin masallacin ne jim kadan bayan jama’a sun fice bayan Sallar Asuba.
A rahotanni sun nuna akalla mutum uku ciki har da yara sun makale a cikin masallacin da ke layin Biba mai yawan shaguna da hada-hadar kasuwanci a garin.
Wani ganau ya ce mutum daya ya samu karaya bayan motar ta kutsa ne ta bayan masallacin inda mata da kananan yara ke Sallah.