Labarai
Kaduna: Sojoji sun kashe ƴan fashin daji a luguden wuta

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce, wasu hare-hare ta sama da jami’an tsaro suka kai, sun yi nasarar hallaka ƴan fashin daji waɗanda ke tserewa yankin Birnin Gwari.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an kashe ‘yan fashin ne yayin da suke tserewa bayan sun kai hari ƙauyen Sabon Layi a yankin.
Haka kuma, Ma’aikatar ta tabbatar da cewa ƴan fashin sun yi harbe-harbe lokacin da suka kai hari yankin na Sabon Layi, tare da kore Shanu da kuma sace kadarorin mazauna yankin.