Connect with us

Labarai

Ƙidayar Jama’a: Ba Za Mu Yi Tambayoyi Akan Addini Da Kabilanci Ba — NPC

Hukumar kidayar jama’a ta kasa (NPC) ta yi karin haske kan cewa shirin kidayar jama’a ba shi da dangantaka da addini da kabilanci.

Hukumar ta yi wannan karin haske ne a ranar Juma’a a Kano lokacin da kwamitin yada labarai na kasa kan kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 ta kai ziyarar ba da shawara ga gidan talabijin na Kasa, a Kano.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ziyarar ta samu jagorancin Alhaji Lai Mohammed, shugaban kwamitin kuma ministan yada labarai da al’adu, wanda babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Dr Garba Abari ya wakilta.

Da yake magana kan rade-radin cewa za a yi wa ‘yan Najeriya tambayoyi kan addininsu da kabilanci, wani mamba a kwamitin, Dokta Isiaka Yahaya, ya ce hukumar ba ta da sha’awar irin wadannan bayanai.

Yahaya, wanda shi ne Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, ya ci gaba da cewa al’amuran addini da kabilanci da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo bashi da tushe balle maka.

“Tun a shekarar 1991 da Hukumar Kidaya ta kasa ke gudanar da kidayar jama’a, ba mu taba yin tambayoyi kan kabilanci da addini ba.

“Ba mu yi shi a 1991 ba, ba mu yi shi a 2006 ba kuma ba za mu yi ba a yanzu.

” Dalili a bayyane yake. Batutuwan biyu suna da matukar muhimmanci kuma suna da karfin karkatar da hankali daga babban batun kidayar,” inji shi.

Hakazalika, Darakta Janar na Muryar Najeriya, Mista Osita Okechukwu, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su kalli kidayar a matsayin wata takara tsakanin kabilu.

“Domin tsare-tsare, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kafin ya bar mulki yana son ya tura fasahar zamani domin gudanar da kidayar al’umma.

“Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed, ya zage damtse wajen yin shiri da albarkatun mu, zai san ainihin ‘yan Najeriya nawa yake jagoranta,” in ji Okechukwu.

A nasa bangaren, Abari ya yabawa mahukuntan NTA da suka taka rawar gani wajen wayar da kan al’umma kan kidayar jama’a.

Ya sake nanata cewa kidayar ta kasance don samun bayanai ne kawai don ci gaban kasa sannan kuma ya bukaci kafafen yada labarai da su taimaka wajen magance tagwayen labaran karya da bayanan bogi.

Babban Manajan NTA Kano, Sani Yusuf, ya bayyana shirin NTA na tallafawa gangamin wayar da kan jama’a kan kidayar jama’a.

Ya ba da tabbacin cewa gidan watsa labarai zai samar da Tallace-Tallace don taimakawa yakin tare da ba da labari game da atisayen.

Jaridar Solacebace ta ruwaito cewa kwamitin ya kuma ziyarci gidajen rediyon Pyramid FM, Kano, Radio Kano da kuma jaridar Triumph. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet