Connect with us

Labarai

Zababben Gwamnan Kano Ya Sake Rubuta Shawara Kan Amfani Da Kudaden Gwamnati

 

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake bayar da Shawarwari ga Jama’a kan zargin yin amfani da kudaden gwamnati wajen sake zaben da za a gudanar a jihar a ranar Asabar 15 ga wata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar ranar Juma’a a Kano.

Sanarwar ta ce: “Muna da sahihan bayanai da ke nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin sakin Naira miliyan 61 ga kananan hukumomin Doguwa, sama da Naira miliyan 60 ga Nasarawa, sama da Naira miliyan 60 ga karamar hukumar Wudil domin gudanar da zabukan.

“Yayin da sauran kananan hukumomi kuma aka sanya sunayensu don karbar daruruwan miliyoyin Naira don gudanar da zaben.”

Sanarwar ta ce an fitar da kudin ne kawai don daukar nauyin ‘yan bangar siyasa don tada zaune tsaye a kan ‘yan jihar da mazauna yankin a lokacin da za a sake zaben jihar.

“Muna sake gargadin dukkan shugabannin kananan hukumomin da ma’aikatan gudanarwar su da su nisanta kansu tare da tabbatar da cewa duk kudaden jama’a da aka saki ba a yi amfani da su ba don haka kuma a mayar da su cikin asusun da ya dace.

Yayin da muke godiya ga mutane nagari da suka fito suka ba mu labarin wasu munanan tsare-tsare da za a zartarta a kan al’ummar jihar Kano gabanin zaben da za a yi a ranar 15 ga Afrilu.

An yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana da hannu a kan wannan badakala zai fuskanci matakin da ya dace a lokacin da ya dace. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet