Labarai
Katsina: NDLEA ta gano gona kin Wiwi guda 3

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta ce, jami’anta sun gano wasu gonaki guda uku da ake shuka tabar wiwi a jihar Katsina.
Mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin gudanarwa a jihar ta Katsina, Halilu Hamidu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce, hukumar ta gano gonakin ne bayan da ta samu bayanan sirri daga wasu mutane.
Haka kuma ya ƙara da cewa, wannan shi ne karon farko da hukumar ta gano irin wannan gonar a kauyen Sobashi na karamar hukumar Dutsi.
Halilu Hamidu ya kuma ce, masu gonar suna amfani da ita ne wajen shuka tabar ta Wiwi inda suke fakewa da noman kayan lambu da suka haɗa da Tattasai da Tumatur.
Haka kuma, Ya ce, hukumar ta cafke waɗanda ke gudanar da wannan mummunar ta’ada.