Labarai
Sallar Idi: Sultan Ya Bukaci ‘Yan Siyasa Da Su Amince Da Sakamakon Da Kotuna Za Su Yanke

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin Addinin Musulunci ta Kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya dora wa ‘yan siyasar da ke neman hakkinsu a gaban kotu da su amince da sakamakon da aka samu da gaskiya.
Abubakar, wanda ya bayyana hakan a jawabinsa na idin karamar sallah ga ‘yan Najeriya ranar Juma’ar nan a jihar Sokoto ya ce: “Zabuka sun zo kuma sun tafi, ya kamata mutane su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin lumana.
“‘Yan siyasa masu neman a yi musu hukunci a kotu su dauki sakamakon da ya dace da kuma goyon bayan duk wanda ya fito domin samar da zaman lafiya, hadin kai da cigaba.”
Sarkin ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki bisa yadda al’ummar musulmin kasar nan suka kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
“A matsayinmu na ‘yan Adam, a kodayaushe muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar rayuwa da lafiya don kasancewa cikin wadanda za su yi murnar wannan babbar rana.
“A lokacin azumin Ramadan, mun koyi abubuwa da dama daga malamanmu, ya kamata mu ci gaba da dawwamar da wadannan darussa domin zama wani bangare na rayuwa.
“Ya kamata a kiyaye karamcinmu ga marasa gata a cikinmu domin mu kyautata dangantakarmu da kuma ci gaba da ƙaunar juna,” in ji shi.
Abubakar ya taya daukacin al’ummar Musulmi a fadin kasar nan, tare da yi wa zababbun shugabannin addu’o’in samun nasara wajen cika alkawuran da suka dauka a yakin neman zabe ga ‘yan kasa.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Ya yi addu’ar Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya da hadin kai, yayin da ya bukaci shugabanni da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da ke kansu. (NAN)