Connect with us

Labarai

Kotu Ta Datse Auren Shekara 18 Da Yi Saboda Rashin Sauke Hakki Da Dukan Matar

Wata kotu mai daraja ta daya da ke Kubwa, a babban birnin tarayya, Abuja, ta tsinke auren shekara 18 na wata mata mai suna Hafizar Saidu da mijinta, Aminu Usman sakamakon rashin kula da ita yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito, alkalin kotun, Malam Yahaya Sheshi ya raba auren nasu ne biyo bayan rokon da Hafizar ta yi wa kotun na raba aure a bisa dalilin rashin kulawa da cutar da ita da batir.

Sheshi ya umurci Hafizer da ta kiyaye “Iddah” wanda itace lokacin jira da za’a yi na tsawon watanni uku kafin a daura wani sabon aure.

Tun da farko, Hafizer ta shaida wa kotun cewa ta auri Aminu ne bisa tsarin shari’ar Musulunci, kuma aurensu Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyar.

“Usman ba ya kula da ni ko iyalanmu, Yana dukana yana zargina da kuskure.

“Ya je wurin iyayena, ya yi musu duka kuma ya yi barazanar kashe iyayena.

Ta ce: “Cin zarafin da mijina yake ya isa haka kuma ina son a raba aurenmu.

Sai dai wanda ake kara ya musanta zargin da ake masa, amma ya amince a raba auren.

“Idan ban sake ta ba, rayuwata na cikin hadari, idan ban sake ta ba ya mai maita.

“Yan uwanta sun lakada min duka kuma an garzaya da ni asibiti domin a yi min magani.

“Ina rokon wannan kotu mai albarka ta biya mata bukatar ta,” in ji Aminu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet