Connect with us

Labarai

Farashin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 42.63% Cikin Shekara Guda – Hukumar NBS

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ce matsakaicin farashin litar man fetur ya karu daga Naira 185.30 a watan Maris din 2022 zuwa Naira 264.29 a watan Maris din 2023.

Ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar farashin man fetur na Maris 2023 da aka fitar a Abuja ranar Litinin din nan.

Ya bayyana cewa a watan Maris din 2023 farashin Naira 264.29 ya nuna karuwar kashi 42.63 bisa farashin Naira 185.30 da aka samu a watan Maris din 2022.

“Idan aka kwatanta matsakaicin farashin da watan da ya gabata na Fabrairu 2023, matsakaicin farashin dillalan ya karu da kashi 0.20 daga Naira 263.76.

“A kan nazarin bayanan jihohi, Imo ta biya mafi girman farashin dillali na Naira 332.67 kan kowace lita, sai Taraba a kan Naida 330.00 sai Borno a kan Naira 324.55.

“Haka zalika, Benue ta biya mafi karancin farashi na Naira 195.00, Plateau ta biya Naira 196.79 sai Nasarawa a kan Naira 197.50,” inji ta.

Bincike daga shiyyar ya nuna cewa yankin Kudu-maso-Gabas ya sami matsakaicin farashi a watan Maris na 2023 a kan Naira 306.00 kowace lita, yayin da Arewa ta Tsakiya ta samu mafi karanci a kan Naira 205.10 kowace lita.

NBS ta kuma bayyana a cikin Rahoton Kallon Farashin Diesel na Maris 2023 cewa matsakaicin farashin dillalan da masu siye ke biya ya karu da kashi 55.90 a kowace shekara.

Ya yi bayanin cewa farashin dillalan ya tashi daga ƙaramin farashi na N539.32 ga kowace lita da aka rubuta a cikin Maris 2022 zuwa mafi girman farashin Naira 836.81 kowace lita a cikin Maris 2023.

“A kowane wata, farashin yana karuwa da kashi 0.47 daga Naira 836.91 ga kowace lita a watan Fabrairun 2023 zuwa matsakaicin Naira 840.81 a cikin Maris 2023,” “in ji ta.

A nazarin bayanan jihar, rahoton ya ce an samu matsakaicin farashin man dizal a watan Maris na 2023 a Bauchi kan Naira 910.46 kan kowace lita, sai Abuja a kan Naira 889.44, sai Adamawa a kan Naira 880.33 kan kowace lita.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, A daya bangaren kuma, an samu mafi karancin farashi a Bayelsa kan Naira 768.04, sai Katsina a kan Naira 779.78, sai Edo kan Naira 797.14 kan kowace lita.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet