Labarai
Hukumar NEMA za ta fara kwaso ƴan Najeriya daga Sudan

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce, za ta fara ɗebo ƴan Najeriya da suka maƙale a Sudan sakamakon rikicin ƙasar daga gobe Talata.
Daraktan ayyukan na musamman a hukumar Olamide Bandele, ne ya sanar da hakan a tattaunawarsa da gidan Talabijin na Channels yau Litinin.
Ya ce, yanzu haka babban Daraktan hukumar ta Mustapha Habib ya na birnin Alkahira na kasar Egypt, inda suka tanadi motocin da za su kwashe mutanen.