Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kwaso Daliban Najeriya Da Suka Makale A Sudan

Gwamnatin tarayya ta fara aikin kwashe daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan. Kamar yadda Daily Post ta ruwiaito.
Akalla mutane 420 ne suka mutu yayin da sama da 3,700 suka jikkata sakamakon kazamin fadan da aka gwabza tsakanin dakarun da ke biyayya ga manyan hafsoshin soji guda biyu a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta saki zunzurutun kudi har Naira milliyan 150 domin daukar hayar motocin bas akalla 40 da za su kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan da yaki ya daidaita ta Alkahira da ke kasar Masar.
An ruwaito cewa wasu daga cikin motocin bas din sun isa ne da safiyar yau Laraba a daidai lokacin da daliban ke shirin komawa Najeriya.