Labarai
Wata Gobara Ta Kone Shaguna Akalla 150 A Babbar Kasuwar Zariya

A kalla shaguna 150 ne gobara ta kone a kasuwar ‘Yan Katako da ke Sabon Gari, Zariya a Jihar Kaduna,kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 1 na safiyar jiya, ta ci gaba har zuwa yammacin ranar Laraba.
Babban jami’in tsaro na kasuwar Hamisu Buhari ya ce gobarar ta fara ne a lokacin da kamfanin wutar lantarki na Kaduna ya dawo da wutar lantarki sannan igiyar wutar lantarki ta tsinko ta fada kan rufin daya daga cikin shagunan.
“Gobarar ta bazu zuwa wasu shaguna a kasuwar,” in ji shi
Buhari ya ci gaba da cewa kokarin jawo hankalin hukumomin kashe gobara a yankin ya ci tura.
“Ni da kaina na je ofishin hukumar kashe gobara ta Kofar Doka. An sanar da ni cewa motar aikinsu ba ta da kyau. Daga nan na wuce harabar Kongo ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) inda aka ce mini an umarce su da kada su yi aiki a wajen harabar jami’ar.
“A karshe na tuntubi hukumar kashe gobara a babbar kasuwar Sabon Gari. Sun bukaci in ba su man Fetur, kafin su mayar da martani,” ya kara da cewa.
A wata hira da shugaban Timbershed dake kasuwar, Alhaji Alin Ashiru, ya kuma alakanta gobarar da tartsatsin wutar lantarki daga sandar wutar lantarki.
Ya bayyana cewa sama da shaguna 150 ne suka kone kurmus sannan kuma an lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.
Da aka tuntubi Shugaban Hukumar KEDCO, Abdul Azeez Abdullahi, ya musanta cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.
Ya ce rahotanni da aka samu sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a daya daga cikin shagunan kasuwar.
Hakazalika, Umar Mohammed, shugaban hukumar kashe gobara na Kofar Doka, Zaria, ya ce motarsu ba ta aiki a sakamakon wani hatsarin da ya faru a baya bayan nan bayan wani aikin ceto a Depot na Sojojin Najeriya.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa tashi gobara a manyan kasuwannin Najeriya ya zama ruwan dare ga mutane a ‘yan kwanakin nan inda aka yi asarar biliyoyin kudi da kadarori.
Kwanan nan a jihar Oyo gobara ta tashi a kasuwar Katako ta Bodija,sai jihar Legas, sannan kuma jihar Kano, gobara ta kone manyan kasuwanni guda uku; Kasuwar Singa da ake sayar da kayayyaki, Kasuwar Kurmi da ake sayar da litattafai da kuma Kasuwar Rimi da ake sayar da kayan daki da kayan kamshi,kazalika gobara ta tashi a kasuwar Monday dake jihar Borno.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Saleh Jilih, ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa dukiyar da gobarar ta lalata ta kai kimanin Naira biliyan 6.