Labarai
Abuja: Ƴan sanda sun ceto mutane 58 daga hannun ƴan garkuwa

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, ta ce, ta samu nasarar ceto mutane 58 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SP Josephine Adeh ta fitar.
Rundunar, ta kuma bayyana cewa, an ceto mutanen ne a dajin Udulu da ke yankin ƙaramar hukumar Gegu ta Jihar Kogi wanda ke da iyaka da dajin Sardauna na Jihar Nasarawa.
Haka kuma ta ce, akwai wasu da aka ceto daga wasu sansanonin masu garkuwa da mutanen da aka gano a wasu wurare a birnin na Abuja.
“A lokacin da barayin suka ga jami’an tsaro karkashin jagorancin ‘yan sanda, sai suka soma harbinsu wanda hakan ya ja aka yi musayar wuta, a cewarta”.
Haka kuma ta ce, “An ci karfin ‘yan bindigar inda suka tsere da raunukan harsasai a jikinsu tare da barin wadanda suka kama.”