Labarai
Kaduna: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴa da jikokin Sarkin Kagarko

Wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai, sun yi dirar mikiya a fadar Mai martaba Sarkin Kagarko da ke yankin kudancin jihar Kaduna Alhaji Sa’ad Abubakar, tare da sace ƴaƴansa 9 da wasu jikokinsa da har ma da ƙarin mutane uku.
Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa ɓata garin sun isa yankin ne da misalin ƙarfe 11:15 na dare.
Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa, ƴan bindigar sun kuma yi awon gaba da amaryar sarkin, sai dai ita ta kuɓuta daga daga hannunsu inda ta dawo gida da kanta.
Haka kuma ganau ɗin ya tabbatar da cewa, cikin ƙarin mutane ukun da ɓata garin suka sace har da wata mata kana suka kuma raunata wani mutum mai suna Audu Kwakulu mazaunin unguwar Pah wanda a halin yanzu yake samun kulawa a asibiti.
Haka kuma ya ce, “Ƴan bindigar sun kuma kashe wani makiyayi a ƙauyen Kuchimi tare da sace kaya a shaguna bakwai a kauyen Janjala duka a karamar hukumar Kagarko – a hanyarsu ta komawa.”