Labarai
An kammala dawo da Ɗaliban Najeriya daga Sudan

Ma’aikatar jin ƙai da kare afkuwar bala’i ta Najeriya da tallafin hukumar agajin gaggawa NEMA da ofisoshin jakadancin Najeriya na ƙasashen Sudan da Masar, sun kammala kwashe ɗaliban Najeriya da suka maƙale a Sudan.
Kafar yaɗa labarai ta BBC, ta ruwaito cewa babban sakatare a ma’aikatar jin kai da kare afkuwar bala’i a Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya shaida mata hakan.
Ya ce, sai da aka bi matakan da suka dace domin tabbatar da kariyar ɗaliban, kafin a fara aiki kwaso su.
Haka kuma ta ruwaito cewa, jami’in ya ce jirgin da ya sauka a ranar Asabar shi ne jirgi na 15 kuma na ƙarshe a jigilar ɗaliban.
Haha Kuma ya ƙara da cewa, kaso 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.