Labarai
Neja: Ƴan bindiga sun sace Dagaci da ƙarin mutane 49

Wasu ƴan bindiga, sun sace Dagacin ƙauyen Fugge, a ke yankin ƙaramar hukumar Rijau ta Jihar Neja Malam Abdullahi Zaure tare da wasu mutane 49.
Rahotonni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai harin ne ranar Juma’ar da ta gabata inda suka yi awon gaba da mutanen waɗanda suka ƙunshi mata da ƙananan yara da kuma maza magidanta.
Haka kuma, Rahotonni sun ce, maharan sun tattara shanu a yankin tare da yin awon gaba da su.
Jaridar Blueprint, ta ruwaito cewar, maharan sun kai hari ƙauyen ne da tsakar rana a kan babura inda suka yi harbe-harbe kan mai uwa da wabi don razana da mutanen yankin.