Labarai
Tinubu ya naɗa muƙami na farko a matsayinsa na shugaban ƙasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa, sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a yau Litinin.
Alake ya dade tare da Tinubu, inda har ta rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru a ƙarƙashin Tinubu da ga 1999 zuwa 2007 a lokacin ya na gwamnan jihar Legas.
Haka kuma shugaban ya nada Ambasada Kunle Adeleke a matsayin zagin shugaban ƙasa.
Ya kuma naɗa shugaban matasan APC na kasa, Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yaɗa labarai na zamani.
Muƙamansu sun fara aiki nan take.