Labarai
Gwamna Zulum zai ɗauki Malamai 5,000 aiki

Gwamnar jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce, zai ɗauki Malamai 5,000 aiki domin fara karatun firamare da sakandare da rana domin magance matsololin cunkoso da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a jawabinsa jim kaɗan bayan ya sha rantsuwar kama aiki a karo na biyu.
Ya ce : “Duk da cewa mun gina sabbin makarantu masu girman gaske tare da fadada makarantun da ake da su da sabbin ajujuwa kusan 1,000, amma har yanzu muna fuskantar matsalar cunkoso a ajujuwa, kuma muna fama da matsalar da dubban yara da ba sa zuwa makaranta”
“Ina mai farin cikin sanar da cewa nan ba da jimawa ba jihar Borno za ta fara tsarin makarantun firamare da sakandare na rana. Na nada kwamitin aiwatarwa da zai tsara hanyoyin da za a fara karatun makarantun la’asar, kuma zai tantance makarantun gwajin da za a zabo daga wasu manyan makarantunmu na Maiduguri da ke da lantarki.”
Zulum ya bayyana cewa bullo da tsarin karatun na yamma zai bukaci karin ma’aikata, don haka ya umurci ofishin shugaban ma’aikata da ya zakulo wasu kwararrun ma’aikatan da a halin yanzu ba sa aiki a sakatariyar gwamnati, wadanda za a horar da su kan sanin makamar aikin.
Gwamnan ya kuma ce za a ɗauki matakan tsaro domin tabbatar da samun nasarar makarantun na yamma, yana mai cewa a wasu lokutan ana iya daukar darasi har zuwa farkon dare.