Labarai
Zamfara: Ƴan bindiga sun sace fiye da ƴan mata 30

Wasu ƴan bindiga da suka kai hari wasu ƙauyuka a Zamfara sun hallaka mutane da dama gami da sace ƴan mata su fiye da 30.
Rahotonni sun bayyana cewa ɓata garin sun kai harin ne a yankin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.
BBC ta ruwaito cewa, ƴan bindigar sun harin ne ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako da tsakar ranar jiya Asabar inda suka kashe fiye da muane ashirin a Sakkiɗa tare da jikkata wasu mutanen.
Haka kuma ta ruwaito cewa, wani mazaunin yankin ya shaida mata cewa, an dauki ƴan mata fiye da 30 a kauyen Gora a yayin da suka tafi yin itace a dajin Ɗaggera.
Ya ce, “ƴan bindigar sun bayar da sanarwa tun kafin sace yaran cewa idan har muna so mu yi noma a Ɗaggera a bana, to sai mun zauna mun yi sulhu da su, kuma mu yi ta sulhu da su amma bamu san dalilin sace mana yaran ba.”
“ Har kawo yanzu dai bamu ji daga garesu a kan yaran ba, amma jami’an tsaro sun bi bayansu sai dai ba wani labari” inji shi.