Labarai
Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Yara Tara Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ceto wasu yara guda 9 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga al’ummar Gora-Namaye da ke karamar hukumar Maradun a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Lahadi.
Ya ce, “A ranar 3 ga watan Yunin 2023, da misalin karfe 20:14, aka samu labari daga Hakimin kauyen Gora-Namaye a karamar hukumar Maradun cewa an kama yara tara da suka hada da maza da mata da iyayensu suka tura su debo itace a daji, kuma ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
“Da samun rahoton, ‘yan sandan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru kuma suka fara aikin bincike da ceto wanda suka kai ga ceto yaran.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa, Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa tuni rundunar ‘yan sandan ta hada wadanda lamarin ya shafa da iyalansu ba tare da wani sharadi ba.
“Har yanzu ana ci gaba da kokarin gano ‘yan bindigar domin gurfanar da su gaban kotu,” in ji Abubakar.
Kamfanin dillancin Labarai Kasa ya ce a ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukan karamar hukumar Maradun inda suka kashe wasu da ba su ji ba ba su gani ba.