Labarai
Kano: An ƙone Adaidaita Sahun wasu da aka zarga da fashin Waya

Wasu fusatattun matasa, sun ƙone wani babur ɗin Adaidaita Sahu a unguwar Ƙofar Famfo da ke jihar Kano.
Matasan sun zargi masu babur ɗin Adaidaita sahun da yunƙurin aikata fashi da makamin wayar salula ga wata mata, waɗanda ba su samu nasara ba.
Matasan dake yankin sun kawo wa matar ɗauki bayan sun hangi ƴan fashin wayar na ƙoƙarin aikata mata fashi.
Hakan ce ta sanya matasan suka bankawa Babur ɗin wuta har sai da ya ƙone.
Hukumomin tsaro dai sun yi kira ga jama’a su daina ɗaukar doka a hannunsu, su bari jami’an tsaron su gudanar da bincike.