Connect with us

Labarai

EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Ma’aikatan Banki Bisa Zargin Sata

Hukumar da ke yiki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa EFCC a ranar Talatar nan ta gurfanar da wasu ma’aikatan banki guda biyu Freeman Jacob da Umar Abdullahi a gaban mai shari’a Akgah Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano.

An gurfanar da matasan biyu bisa tuhumarsu da laifuka uku da suka hada da hada baki da satar kudi.

Hukumar ta kuma gurfanar da wasu mutane biyu Ahmad Bashir da Abdulhakim Musa wanda aka fi sani da Gandu a gaban kuliya bisa laifin yin aiki tare da mitanen biyu a shekarar 2020.

A cewar hukumar wadanda ake zargin sun hada baki ne a tsakaninsu wajen samar da katin cirar kudi na ATM da sunan wani Alhji Sani Muntari.

Haka kuma suka yi amfani da katin wajen sace makudan kudi Naira miliyan 20,000 a bankinsa.

Daya gada cikin tuhume-tuhumen da ake musu ta ce “Kai Freeman Austin Jacob, da Umat Abdullahi a wani lokaci a watan Fabrairun 2020 a Kano da ke yanki karkashin wannan kotu mai girma, kun hada kai da Ahmad Bashir da Abdulhakim Musa kan wajen samar da katin ATM”

Kun yi wannan abu daga asusun ajiyar bankin kasuwanci mallakin wani Alhaji Sani Muntari ba tare sa sani ko izinin wannan abokin ciniki ba, kuma laifin da za a yi hukuncinsa a karkashin sashi na 14 (7) na dokar intanet.

Wadanda ake tuhumar sun aikata wannan zamba ne ta hanayar amfani da ka layin waya mai asusun ajiya, wanda Bashir da ake tuhuma na uku ya sace, aka samar da katin ATM tare da taimakon wadanda ake kara na daya da na biyu.

Bincike ya gani wasu kudade da aka samu na satar a asusun bankin wanda ake kara na hufu, Abdulkarim Musa abokin wanda ake kara na uku Ahmad Bashir.

Sai dai wadanda ake kara sun musanta aikata laifin, kuma alkalin ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa 26 ga watan Yuni domin fara sauraren karar da bukatar bada beli

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet