Labarai
NJC Ta Amince A Binciki Wasu Alkalan Najeriya Guda Bakwai

Majalisar shari’a ta kasa, NJC, ta amince da gudanar da cikakken binciken kan wasu alkalai bakwai
Daukar matakin ya biyo bayan taron kwanaki biyu da Kungiyar lauyoyin da ke da hurumin ladabtar da jami’an shari’a bisa doka ta gudanar a ranakun 14 da 15 ga watan Yuni
NJC tace an yi watsi da karar da aka shigar kan wasu mutane 26 da suka hada da mai shari’a Mary Peter Odili mai ritaya
Majalisar shari’a ta kasa, NJC, ta amince da gudanar da cikakken binciken kan wasu alkalai bakwai da ake zargi da aikata laifukan cin hanci da rashawa.
Kungiyar lauyoyin da ke da hurumin ladabtar da jami’an shari’a a kasar bisa doka, ta ce ta kafa kwamitin binciken alkalan, bayan wani taron kwanaki biyu da ta gudanar a ranakun 14 da 15 ga watan Yuni.
Taron, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na hukumar ta NJC, Mista Soji Oye, ya kasance karkashin jagorancin alkalin alkalan Najeriya, CJN, Mai shari’a Kayode Ariwoola, wanda ya zama shugaban majalisar.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki a fannin shari’a ke neman a gudanar da cikakken bincike kan zargin da wani dan majalisar tarayya da kuma mijin tsohuwar shugabar kotun daukaka kara, wanda ya tuhumi bangaren shari’a.
Kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, ta bayyana a matsayin abin mamaki, ikirari da Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi a bainar jama’a, na cewa ya rinjayi hukuncin da matarsa, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, ta yanke, a lokacin da ta kasance shugabar kotun daukaka kara.
Yayin da yake yin Allah wadai da furucin tuhumar da Sanata Bulkachuwa ya yi a wani zama na nuna rashin amincewa da aka yi wa Majalisar Dattawa ta 9, NBA, wadda ita ce kungiyar lauyoyi a kasar, ta bukaci a gudanar da cikakken bincike.
“A kan haka ne nake kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka masu alaka (ICPC), da su gaggauta gayyato Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa domin yi masa tambayoyi sannan a ci gaba da gurfanar da shi a gaban kuliya,” in ji shugaban NBA, Mista Yakubu Maikyau, SAN.
A halin da ake ciki, duk da cewa NJC ba ta bayyana sunayen alkalan da ake bincike ba, amma ta bayyana cewa “Jami’an shari’a ne daga kotun daukaka kara da manyan kotunan Jihohi.”
Majalisar ta ce ta yi la’akari da rahotannin kwamitocin bincike daban-daban da kwamitocin tantance korafe-korafe kan korafe-korafen da aka rubuta a kan wasu jami’an shari’a 33 daga kotun daukaka kara da ta manyan kotuna, sannan ta amince da shawarar kwamitin cewa alkalan bakwai na da tambayoyi da za su amsa.
Duk da haka, NJC ta bayyana cewa an yi watsi da karar da aka shigar kan wasu mutane 26 da suka hada da mai shari’a Mary Peter Odili mai ritaya.
Bugu da kari, NJC ta ce ta ba da shawarar jami’an shari’a 37 ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnoni bakwai, domin a nada su a matsayin alkalan kotun daukaka kara, shugabannin kotuna da alkalan babbar kotu da kotunan daukaka kara ta Kwastomari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Sanarwar ritayar jami’an shari’a na kotunan tarayya da na jihohi tara majalisar ta samu kuma ta lura.”