Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano Ya Jaddada Aniyarsa Ta Kara Dankon Alakar Kano Da Faransa

 

Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na inganta dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin jihar Kano da kasar Faransa.

Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a wata ganawa da jakadan Faransa a Najeriya a fadar gwamnatin jihar a ranar Juma’a.

Wanda ya wakilci Gwamnan, Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana irin kokarin da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wajen kulla alaka da gwamnatin kasar Faransa.

Kwamared Gwarzo ya yi tsokaci na musamman kan yadda Sanata Kwankwaso ya kafa makarantun sakandare domin koyon Faransanci a garin Madobi da wasu biyu a Jamhuriyar Nijar.

A jawabinta, jakadiyar Faransa a Najeriya Emmanuelle Blatmann, ta bayyana cewa ziyarar da tawagar ta kai Kano na da nufin gabatar da ayyukan raya kasa iri-iri ga gwamnatin jihar da nufin samar da ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Blatmann ta kuma yi nuni da cewa, gwamnatin Faransa ta dade tana yin hadin gwiwa a fannin noma a kamfanoni masu zaman kansu, inda ya jaddada inganta ilmin fasahohin aikin gona da koyon sana’o’i ga mata.

Blatmann ta bayyana cewa gwamnatin Faransa ta hannun hukumar raya kasashe ta kasar Faransa ta zuba kudi kusan Euro biliyan uku a wasu ayyuka masu amfani ga ‘yan Najeriya da jihar Kano ke cin gajiyar shekaru 12 da suka gabata.

Wadannan ayyuka sun hada da aikin samar da ruwan sha na birni, aikin motsa jiki, ayyukan makamashi, ayyukan samar da ilimi, aikin sufuri da neman gyara/ farfado da cibiyar al’adun Faransa ta Kano, hanyar samun damar shiga karkara da aikin noma (RAAMP) da dai sauransu.

Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo, a madadin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar wa jakadan Faransa cewa gwamnatin jihar Kano za ta yi nazari sosai a kan dukkan ayyukan da aka tsara.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet