Connect with us

Labarai

Plateau: An sanya dokar hana zirga-zirga a Mangu

Shugaban ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato Markus Artu, ya sanya dokar hana zirga–zirgar jama’a ta tsawon sa’o’i 24.

Hakan dai ya biyo bayan zaman ɗarɗar da ake fama da shi a sassan ƙaramar hukumar ta Mangu a baya-bayan nan.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, shugaban ƙaramar hukumar, ya sanya dokar ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hanunsa da aka fitar yau Litinin.

Sanarwar ta ruwaito cewa, dokar ta ƙunshi hana zirga-zirgar dukkan ababen hawa na tsawon sa’a 24 a yankin har sai abin da hali ya yi.

“Ba a son ganin kowa yana zirga-zirga a yankin, sai dai jami’an tsaro ko kuma wadanda aikinsu ya zama wajibi ga al’umma,” in ji sanarwar.

Matakin sanya dokar na zuwa ne bayan da aka sami wasu munanan hare-hare kwanakin baya.

Haka kuma ta ruwaito cewa, hare-haren dai sun yi sanadin asarar rayukan sama da mutum 150 da dukiyoyi masu tarin yawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet