Labarai
Gwamna Abba Kabir ya gana da Limamai da mahaddata

Gwamnan Kano Abba kabir Yusuf, ya gana da Limaman masallatan Juma’a, da kuma mahaddata Alqur’ani mai girma da kuma majalisar Malaman jihar Kano
Taron Wanda aka gudanar dashi Adakin taro na Africa House, a gidan gwamnati, a cikin jawabinsa Abba kabir ya ja hankalin Malaman a kan fadar abinda suke da hujja akan sa idan sun hau mumbarin jummaa,
sannan ya yi kira a gare su da su sauke nauyin da Allah ya dora musu amatsayin su na jagororin al’umma,
sannan yabaiyana musu irin dalilan da gomnatin sa ta rushe wasu gine-gine da wasu su ke ta yin surutu a kansa musamman masallacin Idi da Otal ɗin Daula da Kuma sansanin Alhazai watau Hajji Camp.
A cikin jawabin nasa ya bayyan yadda wasu suka mallaka wa kansu da ƴaƴansu wadannan filaye
Haka kuma gwamnan nan yayi bayani Mai tsawo kan ilar bada wadannan gurare
Haka kuma, Gwamnan, ya ce, gwamnatinsa ta samu dimbin nasarori cikin kwanaki 22 da kafuwarta.