Connect with us

Labarai

Masu Kadarorin Da Aka Yiwa Alamar Rugujewa Sun zargi Gwamnatin Kano

Mamallaka gine-ginen da aka sanya wa alamu domin rugujewa a kan hanyar BUK a cikin birnin Kano da Hukumar tsara birane ta Kano (KNUPDA) ta yi sun zargi gwamnati da yin aiki biyu.

Jaridar KakakiHausaTime ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta hannun KNUPDA a ranar Juma’a ta kaddamar da sanya alamar rushe gine-ginen daga mahadar Dan’agundi zuwa mahadar WTC da makarantar FCE domin rusa su inda ta bayyana su a matsayin haramtattun gine-gine saboda an gina su ne a kan tsohon katangar ganuwar Kano.

Hakazalika, galibin takardun shaidar zama da kuma amincewa da ginin da SOLACEBASE ta gani sun samu sa hannun tsohuwar gwamnatin gwamna Abdullahi Ganduje.

Shugaban kungiyar, Alhaji Ismaila Bello ya yi wannan zargin a ranar Asabar din nan a wani taron manema labarai, da aka gudanar a Kano.

Bello ya ce gwamnati ba ta yi musu adalci ba ta hanyar sanya wa kadarorin alamar da za a rusa su domin an bi ka’ida wajen samun filayen.

Ya ce mafi yawansu sun sayi filayen ne daga hannun mutanen da gwamnati ta rabawa filayen kamar marigayi Bashir Tofa, Wada Aliyu Gaya, Abdulazeez Ganduje da Muhuyi Magaji Rimingado da dai sauransu.

”Ku kalli wannan kasar mai lamba 25 , daura da Kano Foundation da farko ta Muhuyi Magaji ce amma a wajensa muka saya. Haka kuma me ya sa ba su yiwa gidan man Aliko da sauran su ba, Bello ya tambaya.

‘’A wannan yanki ne suka zarge mu da yin gini a kan tsohuwar katangar ganuwar birnin, Sanata Rabi’u Kwankwaso yana da filaye a nan da gine-gine a kansu, ba su yi alama ba, haka Abdullahi Ganduje da sauran su.

“Ma’ana Gidan Murtala da kansa ya tafi kamar yadda aka gina shi a tsohuwar katangar ganuwar Kano da kuma hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta yan Sanda (MTD) da aka amince da ita a wa’adin mulki na biyu na Rabiu Kwankwaso.”

Lokacin da SOLACEBASE ta tuntubi Barista Muhuyi Magaji Rimigado, dangane da batun rabon, ya tabbatar wa majiyarmu cewa filin da aka ba shi a wurin ba a tsohuwar katangar ganuwar garin yake ba.

”Eh an ba ni fili a wurin da ake magana amma nawa a wajen tsohuwar katangar ganuwa birnin ne. Ina da hakkin a ba ni fili kamar kowane dan Kano kuma dan Najeriya, ”in ji Muhuyi.

Har ila yau, a kan zargin aiki biyu, Manajan Daraktan KNUPDA, Arc. Ibrahim Yakubu ya shaida wa majiyarmu cewa maganar ba gaskiya ba ce.

Yakubu ya ce wasu gine-ginen da ke jikin tsohon katangar birnin da mutane ke ganin ba haka ba ne, domin kuwa sai an gudanar da aikin tantance takarfun kowane da aka ware.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet